Ba zamu hana Sanata Omo-Agege shiga majalisa bay au – Majalisar Dattawa

Ba zamu hana Sanata Omo-Agege shiga majalisa bay au – Majalisar Dattawa

An dakatad da sanata mai wakiltan Delta ta tsakiya, Ovie Omo-Agege, na tsawon kwanaki 90, amma kotu ta yanke hukuncin cewa majalisa ba tada hurumin dakatad da shi.

A wani jawabi da kakakin majalisan dattawa, Sabi Abdullah ya saki, yace lauyoyi sun basu shawara a kan shari’ar da kotu ta yanke kan watsi da dakatarwan Sanata Omo-Agege.

Justice Nnamdi Dimgba na babban kotun tarayya da ke zaune a Abuja ya yi watsi da dakatarwan da majalisa ta yiwa Sanata Omo-Agege a ranan Alhamis da ya gabata.

Ba zamu hana Sanata Omo-Agege shiga majalisa bay au – Majalisar Dattawa

Ba zamu hana Sanata Omo-Agege shiga majalisa bay au – Majalisar Dattawa

Mr Dimgba yace wannan shawara da majalisa ta yanke na dakatad da shi ya sabawa kundin tsain mulkin Najeriya.

Bisa ga wannan shari’a, wani hadimin shugaban majalisan dattawa, yace majalisan ta daukaka wannan kara kuma ta bukaci a dakatad da zantar da wannan oda.

KU KARANTA: ‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma - Inji ‘Yan Shi’a

Amma a ranan Litinin, Sanata Agege ya ce hakan ba zai hanashi zuwa majalisa ba. A jawabin majalisar, ta ce za ta bari Sanata Agege za shiga majalisa domin nuna da’a ga kotu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel