An lalata motocci yayin arangama da 'yan Shi'a su kayi da 'yan sanda a Abuja

An lalata motocci yayin arangama da 'yan Shi'a su kayi da 'yan sanda a Abuja

- 'Yan Shi'a sun cigaba da gudanar da zanga-zanga a ranar 14 ga watan Mayu a kan tsare shugabansu Shiekh Ibrahim El-Zakzaky

- Zangar-zangar ya kazance a yayin da jami'an yan sanda sukayi yunkurin tarwatsa masu zanga-zangar

- An lalata motocci masu yawa kana wani jami'an dan sanda ya raunana sakamakon duwatsu da matasan shi'an suke harbawa yan sandan

Matasan kungiyar Islamic Movenment of Nigeria (IMN) wanda akafi sani da Shi'a sun sake gudanar da wata zanga-zanga a jiya Litinin 14 ga watan Mayu inda daga bisani sukayi arangama da Yansanda a haraban babban sakatariyar Abuja.

Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, matasan masu zanga-zanga kan cigaba da tsare shugabansu, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky sun tare hanya inda suka rika barzana ga masu ababen hawa tare da lalata motocci da dama.

An lalata motocci yayin arangama da 'yan Shi'a su kayi da 'yan sanda a Abuja

An lalata motocci yayin arangama da 'yan Shi'a su kayi da 'yan sanda a Abuja

KU KARANTA: Jihohi 5 da suka fi sauran yawan albarkatun man fetur a Najeriya

Wani ganau da ya nemi a sakaya sunansa ya ce wani jami'in dan sanda mai mukamin DCO a sakatariyar tarayya na Abuja, Linus Ogar ya samu rauni a fuskansa sakamakon duwatsu da matasan suka rika jefewa yan sandan.

An ce an garzaya da Ogar cikin harabar sakatarayar tarayya da ke Abuja inda daga nan aka tafi dashi wani asibiti don yi masa magani.

Wani wanda abin ya faru a idanunsa, Bola Saliu, ya yi ikirarin cewa matasan Shi'an ne suka yiwa Ogar rauni da duwatsu. "Ya samu rauni mai tsanani sakamakon duwatsu da masu zanga-zangar suka jefe shi da su. Hakan yasa aka garzaya dashi asibiti saboda raunukan nashi sunyi tsanani."

Daga bisani hukumar Yansandan ta aike da wasu jami'an don taimakawa wanda suke kokarin tarwatsa masu zanga-zangar kuma an kama wasu daga cikin su.

Wani direba mai suna Joshua wanda aka lalata wa mota kirar Acura SUV ya ce yan sandan sun jefawa masu zanga-zangar barkonon tsohuwa wanda hakan yasa su kuma suka yiwa yan sandan ruwan duwatsu har suka fasa masa gilashin mota.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel