Wani dan Shi'a na gab da lashe zabe

Wani dan Shi'a na gab da lashe zabe

Hadakar da tsohon shugaban mayakan shi'a ke jagoranta a Iraqi, Moqtada al-Sadr, na kan hanyar lashe zaben kasar da aka gudanar a karshan mako, bayan sanar da sama da kashi 90 na kuri'un da aka kada a zaben

Wani dan Shi'a na gab da lashe zabe

Wani dan Shi'a na gab da lashe zabe

Hadakar da tsohon shugaban mayakan shi'a ke jagoranta a Iraqi, Moqtada al-Sadr, na kan hanyar lashe zaben kasar da aka gudanar a karshan mako, bayan sanar da sama da kashi 90 na kuri'un da aka kada a zaben.

DUBA WANNAN: El-Rufai yayi na'am da zaben kananan hukumomin jihar Kaduna

Mista Sadr dai bai tsaya takarar Firaminista ba, sai dai nasarar maki da hadakarsa zata samu zai bashi damar yin tasiri wajen lashe zaben wanda zai bashi damar samun wannan mukami.

Wani jami'in hukumar yada labarai yace wannan babban nasara ce ga Moqtada al-sadr, wanda ya bayyana kansa a matsayin fitacce dake adawa da cin hanci da rashawa, hakazalika yayi fice wajen nuna adawa ga kasar Amurka da kuma kasar Iran.

Firaministan mai-ci Haider Abadi, ya gaza kai wa abinda aka yi tsanmani, duk kuwa da nasarar da kasar Iraqi tayi akan kungiyar 'yan ta'adda ta IS a karkashinsa.

Al-Abadi ya bukaci dukkanin jam'iyyun siyasar kasar da su mutunta sakamakon zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel