Gwamnatin Buhari ba abinda ta tsinanawa Al'umma - Shekarau

Gwamnatin Buhari ba abinda ta tsinanawa Al'umma - Shekarau

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana fuskantar zazzafar adawa a dai dai lokacin da zaben 2019 ke kara kusantowa

- Tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau, yace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata tabuka wani abu na azo a gani ba a tsawon fiye da shekaru uku data shafe tanayi akan mulkin

Gwamnatin Buhari ba abinda ta tsinanawa Al'umma - Shekarau

Gwamnatin Buhari ba abinda ta tsinanawa Al'umma - Shekarau
Source: Twitter

Tsohon gwamnan jihar Kano Mallam Ibrahim Shekarau, yace gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari bata tabuka wani abu na azo a gani ba a tsawon fiye da shekaru uku data shafe tanayi akan mulkin.

A wata hira da yayi da manema labarai tsohon gwamnan Malam Ibrahim Shekarau yace yadda gwamnatin Buhari take tafiyar da mulkin ta tamkar bata san abinda take yi ba.

DUBA WANNAN: An yi kira ga musulmin duniya dasu zama tsintsiya madaurinkin daya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana fuskantar zazzafar adawa a dai dai lokacin da zaben 2019 ke kara kusantowa.

Tsohon Gwamnan jihar ta Kano kuma jigo a jam'iyyar adawa ta PDP yace zai sauya fasalin yadda ake gudanar da mulkin kasar nan idan har ya zama shugaban kasar Najeriya.

Sannan ya musanta zarge-zargen da ake yi mishi na cewa yana da hannu a rarraba kudaden da ake zargin an wawure gabannin zaben 2015 a lokacin mulkin Jonathan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel