Nigerian news All categories All tags
Canji: Gwamnatin Buhari ta mayar da 'yan gudun hijira dubu 8 gida

Canji: Gwamnatin Buhari ta mayar da 'yan gudun hijira dubu 8 gida

Babban jami'in hukumar agajin gaggawa ta gwamnatin tarayya dake kula da shiyyar Arewa maso gabas mai suna Bashir Garga ya bayyana cewa kawo yanzu dai kimanin 'yan gudun hijira dubu takwas ne hukumar su ta maida gidaddajin su a karamar hukumar Bama.

Bashir yayi wannan ikirarin ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a garin Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda kuma ya bayyana cewa dukkan wannan nasarar da suka samu na daga kyakkyawan shugabancin shugaba Muhammadu Buhari.

Canji: Gwamnatin Buhari ta mayar da 'yan gudun hijira dubu 8 gida

Canji: Gwamnatin Buhari ta mayar da 'yan gudun hijira dubu 8 gida

A wani labarin kuma, Rundunar sojin Najeriya ta bayyana samun nasarar kubutar da wani tsoho daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram tare kuma da kashe manyan kwamandojin mayakan har biyu yayin wani kazamin artabu a tsakanin su.

Kamar dai yadda muka samu daga mai magana da yawun rundunar ta Lafiya Dole da ke a yankin arewa maso gabashin kasar Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa anyi artabun ne a ranar Talatar da ta gabata a wani kauyen Gobara dake a jihar ta Borno.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel