Sanata Shehu Sani na cigaba da fuskantar matsin lamba kan ya koma PDP

Sanata Shehu Sani na cigaba da fuskantar matsin lamba kan ya koma PDP

Rahotannin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, PDP a takaice na cigaba da zawarcin Sanata Shehu Sani da ke wakiltar mazabar jihar Kaduna ta tsakiya ya dawo cikin ta.

Mun samu kuma dai cewa Sanatan na ta fuskantar matsin lamba daga bangarori da dama kuma mabanbanta da suka hada da kungiyoyin matasa da ma dattijai daga jam'iyyar ta PDP.

Sanata Shehu Sani na cigaba da fuskantar matsin lamba kan ya koma PDP

Sanata Shehu Sani na cigaba da fuskantar matsin lamba kan ya koma PDP

KU KARANTA: Wani mutum ya kai beraye 5 wurin hukuma

Legit.ng ta samu haka zalika cewa yanzu haka ma dai wata kungiyar matasa ta jam'iyyar PDP din a mataki na tarayya ta PDP National Youth League ta fitar da sanarwa dauke da sa hannun shugaban ta Honourable Inioribo Tamunotonye da kuma jami'ar hulda da jama'a ta kungiyar Zainab Al-Amin suna rokon sa ya bar APC din.

A wani labarin kuma, Kawunan tsaffin 'yan jam'iyyar PDP da suka koma jam'iyyar APC ana gaf da zaben shekarar 2015 ya rarrabu biyo bayan wata budaddiyar wasika da suka yi wa shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar ta APC inda suka zargi cewa an maida su saniyar ware.

Sai dai a wata budaddiyar wasika dake zaman martani ga fitattun 'yan siyasar, daya daga cikin tsaffin 'yan PDP kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya rubuta, ya bayyana cewa zargin na su bai da tushe balle makama.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel