Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram 2

Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram 2

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana samun nasarar kubutar da wani tsoho daga hannun 'yan ta'addan Boko Haram tare kuma da kashe manyan kwamandojin mayakan har biyu yayin wani kazamin artabu a tsakanin su.

Kamar dai yadda muka samu daga mai magana da yawun rundunar ta Lafiya Dole da ke a yankin arewa maso gabashin kasar Kanal Onyema Nwachukwu ya bayyana cewa anyi artabun ne a ranar Talatar da ta gabata a wani kauyen Gobara dake a jihar ta Borno.

Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram 2

Da dumin sa: Dakarun sojojin Najeriya sun kashe manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram 2

Legit.ng ta samu cewa haka ma rundunar sojin ta yi nasarar kwato muggan makamai masu yawa daga hannun 'yan ta'addan.

A wani labarin kuma, Kawunan tsaffin 'yan jam'iyyar PDP da suka koma jam'iyyar APC ana gaf da zaben shekarar 2015 ya rarrabu biyo bayan wata budaddiyar wasika da suka yi wa shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar ta APC inda suka zargi cewa an maida su saniyar ware.

Sai dai a wata budaddiyar wasika dake zaman martani ga fitattun 'yan siyasar, daya daga cikin tsaffin 'yan PDP kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya rubuta, ya bayyana cewa zargin na su bai da tushe balle makama.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel