Bango ya tsage: Kawunan tsaffin 'yan PDP da suka koma APC ya rarrabu

Bango ya tsage: Kawunan tsaffin 'yan PDP da suka koma APC ya rarrabu

Kawunan tsaffin 'yan jam'iyyar PDP da suka koma jam'iyyar APC ana gaf da zaben shekarar 2015 ya rarrabu biyo bayan wata budaddiyar wasika da suka yi wa shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar ta APC inda suka zargi cewa an maida su saniyar ware.

Sai dai a wata budaddiyar wasika dake zaman martani ga fitattun 'yan siyasar, daya daga cikin tsaffin 'yan PDP kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya rubuta, ya bayyana cewa zargin na su bai da tushe balle makama.

Bango ya tsage: Kawunan tsaffin 'yan PDP da suka koma APC ya rarrabu

Bango ya tsage: Kawunan tsaffin 'yan PDP da suka koma APC ya rarrabu

KU KARANTA: Ni na koyawa Kwankwso sa jar hula - Ganduje

Legit.ng ta tuna cewa a satin da ya gabata ne dai tsaffin 'yan PDP din suka rubutawa shugaba Buhari da kuma shugabannin 'jam'iyyar APC takarda inda kuma suka bayar da wa'adin kwana bakwai ya saurare su ko kuma su dauki mataki.

A wani labarin kuma, Shugabannin majalisar dattijai a Najeriya a daren jiya sun yanke shawarar dage dakatarwar da suka yi wa hatsabibin Sanatan nan daga jihar Delta watau Sanata Ovie Omo-Agege da suka zarga da jagorantar katti tare da sace sandar girman majalisar a kwanan baya.

Kamar dai yadda muka samu, majalisar ta ce ta dage dakatarwar da tayi Sanatan har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukuncin dake a gabanta game da korar da tayi masa.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel