Dole-uwar-naki: Majalisar dattijai ta dage dakatarwar da tayi wa Sanata Ovie Omo-Agege

Dole-uwar-naki: Majalisar dattijai ta dage dakatarwar da tayi wa Sanata Ovie Omo-Agege

Shugabannin majalisar dattijai a Najeriya a daren jiya sun yanke shawarar dage dakatarwar da suka yi wa hatsabibin Sanatan nan daga jihar Delta watau Sanata Ovie Omo-Agege da suka zarga da jagorantar katti tare da sace sandar girman majalisar a kwanan baya.

Kamar dai yadda muka samu, majalisar ta ce ta dage dakatarwar da tayi Sanatan har zuwa lokacin da kotun daukaka kara zata yanke hukuncin dake a gabanta game da korar da tayi masa.

Dole-uwar-naki: Majalisar dattijai ta dage dakatarwar da tayi wa Sanata Ovie Omo-Agege

Dole-uwar-naki: Majalisar dattijai ta dage dakatarwar da tayi wa Sanata Ovie Omo-Agege
Source: Depositphotos

KU KARANTA: Ba wanda ya isa in ci amanar Buhari - Buratai

Legit.ng dai ta tuna cewa majalisar a kwanan baya ta dakatar da Sanata Ovie Omo-Agege ne har na tsawon kwanaki 90 bisa abin da ta kira karya dokokin ta da yayi.

A wani labarin kuma, Kawunan tsaffin 'yan jam'iyyar PDP da suka koma jam'iyyar APC ana gaf da zaben shekarar 2015 ya rarrabu biyo bayan wata budaddiyar wasika da suka yi wa shugaba Muhammadu Buhari da jam'iyyar ta APC inda suka zargi cewa an maida su saniyar ware.

Sai dai a wata budaddiyar wasika dake zaman martani ga fitattun 'yan siyasar, daya daga cikin tsaffin 'yan PDP kuma tsohon gwamnan jihar Nasarawa Sanata Abdullahi Adamu ya rubuta, ya bayyana cewa zargin na su bai da tushe balle makama.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel