Jahohi 4 da jam'iyyar APC ta rabe 2 sakamakon zaben shugabanni

Jahohi 4 da jam'iyyar APC ta rabe 2 sakamakon zaben shugabanni

Ita dai siyasa daman kamar yadda kwararru a cikin ta suke fadi ba'a rabata da rikice rikice amma dai da alama na jam'iyyar APC mai mulki na neman ya gagari kundila musamman ma yadda a kullum ake ta dada kara samun rarrabuwar kawuna a tsakanin 'ya'yan ta a jahohi da dama.

Kamar dai yadda muka samu, jam'iyyar a jahohi da dama ta samu rarrabuwar kai biyo bayan zabukan shugabannin ta da aka gudanar a satikan da suka gabata a dukkan mazabu da kuma kananan hukumomi.

Jahohi 4 da jam'iyyar APC ta rabe 2 sakamakon zaben shugabanni

Jahohi 4 da jam'iyyar APC ta rabe 2 sakamakon zaben shugabanni

Legit.ng ta samu cewa yayin da zabukan suka gudana cikin kwanciyar hankali a wasu jahohi, a wasu kuwa an gudanar da zabukan ne ma a wurare biyu wanda hakan ya jaza samar da shugabanni kala biyu.

Haka ma wasu jahohin zabukan gagara suka yi inda sai dai aka dage gudanar da zabukan har sai nan gaba.

Ga dai wasu daga cikin jahohin da jam'iyyar ta rabu biyu nan:

1. Adamawa

2. Kano

3. Zamfara

4. Filato

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Mailfire view pixel