Da dumi-dumi: Uwargidan Donald Trump na fama da ciwon koda, an yi mata aikin tiyata yau

Da dumi-dumi: Uwargidan Donald Trump na fama da ciwon koda, an yi mata aikin tiyata yau

Uwargidan shugaban kasan Amurka, Melania Trump na fama da ciwon koda yayinda akayi mata aikin tiyata yau a asibitin Walter Reed National Military Medical da ke birnin Washington DC game da jawabin da ofishinta suka saki.

Melania Trump ta kasance tana fuskanta matsalan koda kuma ya tsananta da ta bukaci aikin tiyata.

Mai Magana da yawunta, Stephanie Grisham, tace: “Da safen nan, uwargidan shugaban kasa, Melania Trump, ta fuskanci aikin tiyata sanadiyar ciwon koda. An samu nasara kuma babu wani matsala.”

" Melania Trump tana asibtin Walter Reed National Military Medical Center kuma da yiwuwan tayi mako daya a kwance. Ana sa ran zata warware domin cigaba da aikin yaran da take yi.

Da dumi-dumi: Uwargidan Donald Trump na fama da ciwon koda, an yi mata aikin tiyata yau

Da dumi-dumi: Uwargidan Donald Trump na fama da ciwon koda, an yi mata aikin tiyata yau

Shugaban kasa Donald Trump bai je asibitin ba yayin aikin. Ana sa ran zai kai ziyara nan ba da dadewa ba. Melania Trump yar shekara 48 ce da haihuwa.

Ita ce uwargidan shugaban kasan Amurka da ta taba fuskanta babban rashin lafiya tun bayan Nancy Reagan a shekarar 1987.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel