Shugabannin da aka yi baya na ne suka samarwa cin hanci wajen zama - Gowon

Shugabannin da aka yi baya na ne suka samarwa cin hanci wajen zama - Gowon

Tsohon Shugaban kasa a mulkin soja, Janar Yakubu Gowon, ya bayyana cewa mai yiwuwa matsayin da ya tsinci kan sa bayan an yi masa juyin mulki cikin 1975, shi ne ya sauya tunanin shugabannin Najeriya dangane da cin hanci da rashawa.

Da ya ke tuna abin da ya afku a shekarar 1975, ya ce a lokacin da aka tsige shi daga mulki, ba shi da komai sai albashin sa.

Gowon ya yi jawabin ne a Taron Kasashen Afrika Renon Ingila kan cin hanci da rashawa, a Abuja, inda har ya yi barkwancin cewa, a lokacin da aka hambarar da shi, bai yi tanadin komai a rayuwar sa ba.

Ya kara da cewa, bayan an tsige shi, wasu daga cikin ma’aikatan sa ne da ya tafi taron Kasashen Afrika da su, suka ji kan sa, su ka ba shi sauran kudin guzirin su, domin ya samu na cefane kafin wani lokaci.

A nan ne ya ce watakila mawuyacin halin da ya tsinci kan sa ne bayan an tsige shi, ya sa idan shugabanni sun hau mulki, sai su yi gagarimin tanadi ta yadda rayuwar su za ta kasance, bayan sun bar mulki.

Daga nan sai ya kara yin nuni da cewa jami’an gwamnatin sa ba su raja’a wajen harkallar cin hanci ba.

“Duk abin da kasar nan ta mallaka a lokacin, na Najeriya ne, hakkin ta ne, na jama’ar ta ne, kuma babu dalilin taba komai a ciki.”

Ya kuma yi takaicin yadda wasu shugabannin kasar nan suka bata wa sauran shugabannin suna, har ake yi musu kudin goro, ana ce musu duk barayi ne.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel