Abun da zai faru da Naira da kuma NNPC idan na zama shugaban kasa - Atiku

Abun da zai faru da Naira da kuma NNPC idan na zama shugaban kasa - Atiku

- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sayarwa ‘yan kasuwa da wani bangare na kamfanin tatar main a Najeriya (NNPC), idan har ya zama shugaban kasa

- Atiku Abubakar yayi bayanin cewa kamfanin na NNPC ya dade a cikin matsalar rashin kulawa a kasar nan

- Wazirin Adamawa yace zai bari Naira ta ringa zagayawa yanda ya kamata domin jawo hankalin masu zuba hannun jari

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, ya bayyana cewa zai sayarwa ‘yan kasuwa da wani bangare na kamfanin tatar main a Najeriya (NNPC), idan har ya zama shugaban kasa.

Atiku yayi bayanin cewa kamfanin na NNPC ya dade a cikin matsalar rashin kulawa a kasar nan.

Abun da zai faru da Naira da kuma NNPC idan na zama shugaban kasa - Atiku

Abun da zai faru da Naira da kuma NNPC idan na zama shugaban kasa - Atiku

Lokacin da yace zantawa da Reuters, Wazirin Adamawa yace zai bari Naira ta ringa zagayawa yanda ya kamata domin jawo hankalin masu zuba hannun jari.

KU KARANTA KUMA: Buhari yayi ta’aziyya ga Fasto Bakare akan mutuwar mahaifiyarsa

Abubakar yace “Ina cikin wadanda sukayi amanna da karamar gwamnati da kuma bangaren ‘yan kasuwar, shiyasa nakeso in bunkasa su, musamman bangaren mai da kuma iskan gas da kuma sashen tattalin arziki kamar na hakon dukiyar kasa da kuma ma’adinai.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel