SDP zata fitar da dantakarar ta daga Arewa - Falae

SDP zata fitar da dantakarar ta daga Arewa - Falae

- Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma ciyaman na jam’iyyar SDP Chief Olu Falae, ya zanta da Peter game da yanayin da kasar take ciki akan zabe mai zuwa

- Falae ya ziyarci dattawan Najeriya domin neman shawararsu game da hanyoyin da za’a bi don magance matsalolin kasar nan

- Falae yace tsohon shugaban kasa na zamanin sojoji Gen. Ibrahim Babangida, yace yana goyon bayan jam’iyyar SDP saboda sauran jam’iyyun adawar biyu sun kasa

Tsohon sakataren gwamnatin tarayya kuma ciyaman na jam’iyyar SDP Chief Olu Falae,ya zanta da Peter Dada game da yanayin da kasar take ciki akan babban zabe mai zuwa.

Falae ya ziyarci dattawan Najeriya domin neman shawararsu game da hanyoyin da za’a bi don magance matsalolin kasar nan, musamman na kashe kashe da ake yawan yi fadin kasar.

Falae yace tsohon shugaban kasa a mulkin soja Gen. Ibrahim Babangida, yace yana goyon bayan jam’iyyar SDP saboda sauran jam’iyyun adawar biyu sun kasa, ya kuma kara da cewa yayi farin ciki da cewa mutane irinmu ne suke jagorancin jam’iyyar.

SDP zata fitar da dantakarar ta daga Arewa - Falae

SDP zata fitar da dantakarar ta daga Arewa - Falae

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, ya bayyana manufarsa inda ya bayyana cewa a yanzu muna karkashin mulkin gwamnati wadda tana kallo ake kashe mutanen kasar amma ta kasa yin komai akan lamarin.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan shi’a dake zanga-zanga sun kora jami’an yan sanda a Abuja

Tabbas zamu fitar da dan takararmu daga arewacin najeriya kila kuma daga arewa maso gashin kasar, ko arewa maso yamma, ko kuma arewa ta tsakiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel