Mutane sama da 1,000 sun jikkata, 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Mutane sama da 1,000 sun jikkata, 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

- Rikicin yankin gabas ta tsakiya ya munana, Mutane da dama sun mutu dubunnai sun samu raunuka da dama

- Rikicin dai ya samo asali ne tun lokacin da kasar Amurka ta bayyana aniyarta ta komar da ofishin jakadancinta zuwa birnin kudus daga Isra'ila

A kalla Mutane sama da 41 ne suka mutu yayinda sama da 1,000 suka jikkata a yau Litinin a lokacin bikin kaddamar da sabon ofishin jakadancin Amurka, rikicin dai ya barke ne sakamakon zanga-zangar da Falasdinawan suke gudanarwa a kan iyakar kasar Isra'ila da yankin Gaza na Falasdinawa.

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Yanzu haka ana cigaba da samun rahoton rasuwar Falasdinawan tun bayan yunkurin da suka yi na kutsawa cikin kasar ta Isra'ila kamar yadda wata Jarida ta kasar Isra’ilan ta rawaito.

Sai dai kuma a rahoton da Gidan Talabijin na Aljazeera ya rawaito, ya ce sama da Mutane 2,000 ne suka samu raunuka, kuma yawancinsu duk yara ne kanana.

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

KU KARANTA: Badakalar naira biliyan 6.3: An dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Filato

Zanga-zangar dai an shafe satittika ana gudanar da ita domin nuna adawa da yunkurin shugaban kasar Amurka Donald Trump na mayar da ofishin jakadancin Amurka daga babban birnin Isra’ila Tel Aviv zuwa babban birnin Kudus, amma sai dai kuma zang-zangar ta rikice ne bayan da Falasdinawa suka yi yunkurin tsallakawa zuwa kasar Isra'ilan.

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Daga cikin manyan bakin da suka halacci bikin kaddamar da ofishin sun hada da Firaministan kasar Yahudawan Isra’ilan Benjamin Netanyahu da Matar shugaban Amurka Melania Trump da ‘yarsa Ivanka da kuma wasu manyan kusoshin gwamnatin Amurkan.

Sojojin Israa’ila dai sun yi amfani da karfi wajen dakatar da Falasdinawan a yunkurinsu na shiga kasarsu ta hanyar amfani da hayaki mai sanya ido hawaye da kuma harsashi. Kamar yadda kafafen yada labarai suka rawaito.

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Mutane sama da 1,000 sun jikkata 41 sun mutu yayin bude ofishin jakadancin Amurka a birnin kudus

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel