Badakalar naira biliyan 6.3: An dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Filato

Badakalar naira biliyan 6.3: An dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Filato

Idanun tsohon gwamnan jihar Filato Jonah Jang sun raina fata a yayin da wata babbar Kotun jihar Filato dake zamanta a gari Jos ta dage zaman sauraron karar da hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC ta shigar da shi, inji rahoton Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito EFCC ta tasa keyar Jang ne zuwa gaban Kotu kan zargin da take masa na yin sama da fadi da wasu makudan kudaden al’ummar jihar dasuka kai naira miliyan dubu shida, da miliyan dari uku, N6.3bn.

KU KARANTA: Musulman Duniya sun nuna bacin ransu ga yadda wata kamfanin giya ta yi amfani da Kalmar shahada

Hukumar na tuhumar Jang da aikata laifuka guda goma sha biyu da suka hada danganci sata da cin hanci da rashawa, wanda suke zargin ya aikatasu ne kimanin watanni biyu kafin ya mika ragamar mulki.

Badakalar naira biliyan 6.3: An dage sauraron shari’ar tsohon gwamnan jihar Filato

Jang Jonah

Sai dai a zaman Kotun na ranar Litinin, 14 ga watan Mayu, Lauyan masu kara, Henti Ajiji ya bukaci Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar Laraba,16 ga watan Mayu don basu damar shigar da kararrakinsu yadda ya kamata.

Nan take lauyan wanda ake kara, Robert Clarke ya soki bukatar lauyoyin EFCC, inda yace basu da kwarewar da ake bukata a wajen duk wani lauya, ya kara da cewa ya ji kunya ace EFCC ta shigar da kara gaban Kotu, amma ta gagara bin hanyoyin da ake bi na sauraron kara.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin, sai mai shari’a Daniel Longji y adage sauraron karar zuwa ranar Laraba, ranar da ake sa ran hukumar EFCC za ta kawo Sanata Jonah Jang gaban Kotu, inda shi kuma lauyansa ya yi alkawarin sama masa beli.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel