Tsaro: Sojojin Sama za suyi Rawar Macijiya a Jihar Taraba

Tsaro: Sojojin Sama za suyi Rawar Macijiya a Jihar Taraba

- A yunkurin Rundunar Sojin sama na kasa wajen tabbatar da tsaro, yanzu haka ta aike da dakaru 150 zuwa yankin Arewa maso gabas

- Jihar Taraba na daya daga cikin jahohin da suke fama da matsalar rashin tsaro, musamman a baya-bayan nan

Biyo bayan nasarar da atisayen Operation Python Dance da Rundunar Sojin Ƙasa suka yi a yankin kudancin Najeriya, yanzu haka Sojojin Sama suma sun ƙaddamar da nasu atisayen.

Tsaro: Sojojin Sama za suyi Rawar Macijiya a Jihar Taraba

Tsaro: Sojojin Sama za suyi Rawar Macijiya a Jihar Taraba

Rundunar Sojin saman dai a jiya Lahadi ta aike da dakarunta har 150 zuwa sabuwar cibiyar agajin gaggawa (QRW) da aka kafa a Nguroje dake ƙaramar hukumar Sardauna ta jihar Taraba.

Dama Rundunar nada sashin bayar da agajin gaggawa a yankin Arewa maso gabas da suka haɗa da Doma a jihar Nassarawa da kuma Agatu ta jihar Benue.

Tsaro: Sojojin Sama za suyi Rawar Macijiya a Jihar Taraba

Tsaro: Sojojin Sama za suyi Rawar Macijiya a Jihar Taraba

A nasa jawabin shugaban rundunar Sojin saman, Air Vice Marshal Sadique Abubakar wanda ya samu wakilcin shugaban sashin aiyuka na rundunar AVM Napoleon Balikira, kira yayi ga sabbin jami'an da su kasance masu bin dokar aiki a koda yaushe yayin gudanar da aikinsu.

KU KARANTA: Sojoji sun kashe wani tsohon soja, sun jefar da gawar sa

"Ya kamata ku sani cewa wannan wata dama ce kasancewar da ku aka fara buɗe sashin agajin ya yankin. Kuma ya zama dole zauna da Mutanen yankin lafiya don hakan zai taimaka muku wajen sauke nauyin dake kanku." A AVM Napoleon Balikira

Kafa irin waɗannan cibiyoyin bayar da agajin gaggawar yunƙuri ne da rundunar take na kawo ƙarshen aiyukan ta'addanci da tada zaune tsaye da ƴan tada ƙayar baya su ke yi a yakin.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel