Tsige kakakin jihar Kano: Yan sanda sun kulle majalisar dokokin jihar

Tsige kakakin jihar Kano: Yan sanda sun kulle majalisar dokokin jihar

- Jami’an yan sanda rike da manyan makamai sun mamaye majalisar dokokin jihar Kano da safen nan.

Rahoton da jaridar Daily Trust ta samu shine an tura yan sandan su kulle majalisar ne tun karfe 2 na dare domin hana yan majalisan dokokin shiga.

Masu sharhi sun bayyana cewa wannan abu ba zai rasa alaka da shirin tsige kakakin majalisar dokokin Kano, Alhaji Yusuf Abdullahi Ata, da wasu shugabannin majalisan ba.

Rahoton ya kara da cewa kakakin majalisar ya bada umurnin dakatad da dukkan ayyukan majalisar har sai bayan Idin babban Sallah.

Da aka tuntubi kakakin hukumar yan sandna jihar, SP Magaji Musa Majia, ya tabbatar da wannan abu.

Yace: “Mun tura jami’an yan sanda majalisan ne saboda tabbatar da doka da oda. Muna bukatan zaman lafiya kuma ba zamu amince da duk wanda zai tayar fa hayaniya ba.”

KU KARANTA: Za'a tsige kakakin majalisar dokokin jihar Kano

Jaridar Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa ana daf da tsige sabon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Abdullahi Yusuf Ata wanda bai cika shekara guda a kan kujerar ba.

‘Yan Majalisar dokokin na Jihar Kano akalla 21 su ka sa hannu da nuna yardar cewa za a tsige Kakakin Majalisar. Yanzu haka dai ya rage mutane 6 kurum ake nema su amince da wannan batu a Majalisa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel