Yadda jihohi 36 suka kasa N593.1bn daga watan Janairu zuwa watan Maris

Yadda jihohi 36 suka kasa N593.1bn daga watan Janairu zuwa watan Maris

- Jihohi 36 na kasar nan sun cire N593.1bn daga asusun ajiya na tarayya a cikin harajin da aka samu a cikin watanni uku na farko a shekarar 2018

- Wadanda ke kan gaba wurin samawa gwamnatin tarayya mafi yawan kudin haraji sune kamfanin tatar main a kasa NNPC, sai kamfanin karbar haraji na tarayya, da kuma hukumar kula da safarar kayayyaki ta kasa (CUSTOMS)

- A watan Janairu jihohin 36 na tarayya sun raba N196.99bn, a wata Fabrairu kuma sun raba N195.25bn, sannan kuma a watan Maris sun raba N200.86bn

Jihohi 36 na kasar nan sun cire kusan N593.1bn daga asusun ajiya na tarayya a cikin harajin da aka samu a cikin watanni uku na farko a shekarar 2018.

NAN ta ruwaito daga birnin tarayya a ranar Asabara, cewa Kwamitin rarraba kudaden da ake bayarwa na gudanar da ayyukan tarayya (FAAC) sun bayyana yanda kason kowace jiha yake a kowane wata.

Wadanda ke kan gaba wurin samawa gwamnatin tarayya mafi yawan kudin haraji sune kamfanin tatar main a kasa NNPC, sai kamfanin karbar haraji na tarayya, da kuma hukumar kula da safarar kayayyaki ta kasa (kwastam), sunfi kowa bawa gwamnatin tarayya kudade wadanda aka samu daga bangarorinsu.

Yadda jihohi 36 suka kasa N593.1bn daga watan Janairu zuwa watan Maris

Yadda jihohi 36 suka kasa N593.1bn daga watan Janairu zuwa watan Maris

A watan Janairu jihohin 36 na tarayya sun raba N196.99bn, a wata Fabrairu kuma sun raba N195.25bn, sannan kuma a watan Maris sun raba N200.86bn.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Abubuwan da baku sani ba game da Maryam Babban Yaro

Rabon anyi ta a tsakanin rassan uku na gwamnati ta hamyar amfani da wata hanyar rabon haraji, inda gwamnatin tarayya tanada 52.68%, sai gwamnatin jihohi tana da 26.72%, sai kuma gwamnatin karamar hukuma tana da 20.60%.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel