Kungiyar SERAP ta kai shugaba Buhari kara a Majalisar Dinkin Duniya sakamakon sabawa hukuncin kotu

Kungiyar SERAP ta kai shugaba Buhari kara a Majalisar Dinkin Duniya sakamakon sabawa hukuncin kotu

- Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa tayi kira ga majalisar dinkin Duniya da tayi gargadi ga shugaba Muhammadu Buhari da yayi taka tsantsan game da kin amincewa da umurnin kotu da gangan

- A wani korafi da kungiyar ta aikawa majalisar dinkin Duniya, a ranar 11, ga watan Mayu na shekarar 2018 ta bukaci a gargadi gwamnatin tarayya game da zabar umurnin da zata bi cikin hukuncin da kotun ta yanke

- Hukumar ta nuna damuwar ta na cewa idan ba’a dauki mataki ba, game da gwamnatin tarayyar da bata bin kowane umurni na kotun zai kawo rikici a cikin dokar kasa

Kungiyar kare hakkin dan adam ta kasa tayi kira ga majalisar dinkin Duniya da tayi gargadi ga shugaba Muhammadu Buhari da yayi taka tsantsan game da kin amincewa da umurnin kotu da gangan.

A wani korafi da kungiyar ta aikawa majalisar dinkin Duniya, a ranar 11, ga watan Mayu na shekarar 2018 ta bukaci a gargadi gwamnatin tarayya game da zabar umurnin da zata bi cikin hukuncin da kotun ta yanke.

Hukumar ta nuna damuwar ta na cewa idan ba’a dauki mataki ba, game da gwamnatin tarayyar da bata bin kowane umurni na kotun “zai kawo rikici a cikin dokar kasa”.

Kungiyar SERAP ta kai shugaba Buhari kara a Majalisar Dinkin Duniya sakamakon sabawa hukuncin kotu

Kungiyar SERAP ta kai shugaba Buhari kara a Majalisar Dinkin Duniya sakamakon sabawa hukuncin kotu

SERAP ta bukaci Garcia-Sayan da yayi amfani da Ofishinsa don tabbatar da cewa shugaba Buhari ya cigaba da bin kowane umurni da kotun ke bayarwa don kare martabar kasar da kuma dokokin kasa.

KU KARANTA KUMA: Kannywood: Abubuwan da baku sani ba game da Maryam Babban Yaro

Cikin abubuwan da kungiyar tayi korafi akansu na umurnin kotun da Buhari yaki girmamawa sune sakin shugaban kungiyar Shi’a, Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenatu, wadanda suke a hannun sojojin Najeriya tun a watan Disamba na shekarar 2015, sai kuma saki mai bayar da shawara ta fanin tsaro ga shugaban kasa Kanal Sambo Dasuki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel