Yajin aiki: Likitoci ba su yarda a biya su daidai da sauran Ma’aikata ba

Yajin aiki: Likitoci ba su yarda a biya su daidai da sauran Ma’aikata ba

- Da alamu dai babu karshen yajin aikin da Ma’aikatan asibiti su ka shiga

- Likitocin kasar sun nuna rashin amincewar su da bukatan abokan aikin su

- Don haka mamaki a cigaba da daukan lokaci ba ayi sulhu da Gwamnati ba

Yanzu haka dai Ma’aikatan asibiti a karkashin Kungiyar JOHESU sun tafi yajin aiki a dalilin wasu alkawura da su kace Gwamnati a saba. Batun dawowa daga yajin aikin ma dai ya kara zama watakila.

Yajin aiki: Likitoci ba su yarda a biya su daidai da sauran Ma’aikata ba

Likitoci sun ce ba za a biya su albashi daya da sauran Ma'aikata ba

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Likitocin kasar ba su yarda a biya su albashi daidai da sauran Ma’aikatan asibiti ba. Kungiyar NMA na Likitcoin Kasar tace ba za ta yarda a daidata albashin kowa a asibiti ba.

KU KARANTA: 'Yan Sanda sun tsare matar wani babban 'dan siyasa

Likitocin Kasar sun bayyana cewa ko a gidan giya akwai babba don haka babu dalilin da zai sa a rika biyan su albashi kamar sauran Malaman asibiti. Kungiyar ta JOHESU kuma tana fada da ba Likitoci mukamai da ake yi.

Bayan nan Likitocin dai sun maida martani game da yunkurin da Malaman asibiti ke yi na ganin an daina nada Likitoci su jagoranci sashen asibitoci. Likitocin dai sun ce su su ka fi dacewa da su shugabancin bangarorin asibiti.

Yanzu haka dai Likitoci ba su yi na’am da bukatun abokan aikin su ba. NMA dai tace za ta goyi bayan a kara shekarun ritayan Ma’aikatan asibiti sannan kuma a biya su wasu kudi da su ke bi amma sauran batun sai dai a kai kasuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel