Ana shirin tsige Kakakin Majalisar Kano Abdullahi Ata

Ana shirin tsige Kakakin Majalisar Kano Abdullahi Ata

- Ana yunkurin tsige Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano

- Kwanaki aka nada Abdullahi Ata bayan tsige Kabiru Rurum

- An zargi Rurum da laifuffuka a lokacin yana rike da kujerar

Wata Majiya mai karfin gaske daga Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ana daf da tsige sabon Kakakin Majalisar dokokin Jihar Kano Abdullahi Yusuf Ata wanda bai cika shekara guda a kan kujerar ba.

Ana shirin tsige Kakakin Majalisar Kano Abdullahi Ata

'Yan Majalisar Kano sun shirya tsige Abdullahi Ata

Jaridar ta kasar ta bayyana cewa ‘Yan Majalisar dokokin na Jihar Kano akalla 21 su ka sa hannu da nuna yardar cewa za a tsige Kakakin Majalisar. Yanzu haka dai ya rage mutane 6 kurum ake nema su amince da wannan batu a Majalisa.

KU KARANTA: Wani Gwamnan APC yayi shekaru 7 a mulki babu albashi

Dokar Kasa dai ta bada damar ‘Yan Majalisa su tsige Shugaban su muddin aka samu akalla biyu-bisa-uku su na goyon-bayan hakan a Majalisar. Tuni dai manyan Majalisar na Kano su ka shirya yin waje da Rt. Hon. Abdullahi Ata daga kujerar sa.

Kamar yadda wani na cikin Majalisar ya bayyanaw Jaridar sun yi nufin tsige Kakakin ne saboda ta tabbata bai san aikin sa ba. Bayan wannan ma dai wani ‘Dan Majalisar yace akwai dalilai da sun fi shurin masaki da su ka za su tsige Yusuf Ata.

Majiyar ta bayyana cewa wani ‘Dan Majalisar na Kano yace ba za su jira sai abubuwa sun cabe sannan su yi wani abu ba. Idan ba ku manta ba dai kwanakin baya Abdullahi Yusuf Ata ya canji Kabiru Alhassan Rurum a kujerar Shugaban Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel