2019: Shugaba Buhari zai yi nasara Inji Minista Chris Ngige

2019: Shugaba Buhari zai yi nasara Inji Minista Chris Ngige

Ministan kwadago na Kasar nan Sanata Dr. Chris Ngige ya bayyanawa wasu ‘Yan Jam’iyyar APC cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne zai sake lashe zabe mai zuwa a 2019 hankali kwance ind yace Buhari zai kawo Anambra.

2019: Shugaba Buhari zai yi nasara Inji Minista Chris Ngige

Minista Ngige yace Shugaba Buhari zai kawo Anambra
Source: Twitter

Ministan ya bayyana wannan ne lokacin da ake rantsar da sababbin Shugabannin Jam’iyyar APC a Garin Ojoto na Karamar Hukumar Idemili a Jihar Anambra. Ngige yace Shugaba Buhari ya cancanci ya zarce a mulki.

Chris Ngige ya bayyanawa shugabannin Jam’iyyar da aka zaba cewa Shugaban kasar yayi kokari a shekaru kusan 3 da yayi yana mulki a Kasar. Dr. Ngige yace kusan kowane bangare Gwamnatin Shugaba Buhari ta taba.

KU KARANTA:

Ministan yake cewa Shugaba Buhari zai samu gagarumar nasara ne ba ta wasa ba a zaben na 2019 inda ya nemi manyan APC a Jihar su yi bakin kokarin su wajen ganin Shugaba Buhari ya samu akalla kashi 70% na Jihar Anambra.

Chris Ngige dai yace an yi zaben Shugabannin Jam’iyyar na APC hankali kwance a Jihar Anambra inda ya yabawa ‘Yan Jam’iyyar. Shi ma Ma’ajin APC na Kasa Cif George Moghalu ya yaba da wannan kokarin da Jam’iyyar tayi.

Dazu kun ji cewa wasu sun koka da zaben da aka gudanar a karshen makon nan a Jihar Kaduna. Wannan karo dai an yi amfani ne da na’ura mai kwakwalwa wajen zaben na Kananan Hukumomi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel