Zaben Ekiti: Dr. Kayode Fayemi zai bar Gwamnatin Shugaba Buhari

Zaben Ekiti: Dr. Kayode Fayemi zai bar Gwamnatin Shugaba Buhari

Bisa dukkan alamu Ministan Ma’adanai na Najeriya Dr. Kayode Fayemi zai bar Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari kwanan nan bayan ya lashe zaben fitar da gwani na Gwamnan Jihar Ekiti a kakashin Jam’iyyar APC.

A karshen makon nan ne Kayode Fayemi ya doke wasu ‘Yan takara sama da 30 daga ciki har da wani mai ba Shugaba Buhari shawara ya lashe tutar Jam’iyyar APC a zaben Gwamnan Ekiti da za ayi a tsakiyar wannan shekarar.

Zaben Ekiti: Dr. Kayode Fayemi zai bar Gwamnatin Shugaba Buhari

Fayemi zai bar kujerar Minista bayan Amina Mohammed da Marigayi Ocholi

Shugaba Muhammadu Buhari da kan sa ta bakin Garba Shehu ya taya Ministan na sa murnar samun tikitin APC. Shugaban Kasa Buhari ya yabawa Kayode Fayemi wanda yace yayi kokari a lokacin da ya rike Gwamnan Ekiti.

KU KARANTA: Ayo Fayose zai dandana kudar sa na zagin Shugaba Buhari

Akwai kishin-kishin din cewa Ministan zai aika takardar murabus daga matsayin Minista a makon nan domin ya fita yakin neman zabe. A 14 ga Watan Yuli ne Dr. Kayode Fayemi zai kara da Mataimakin Gwamna Ayo Fayose na PDP.

Idan ba ku manta ba dai kafin nan dama Ministan ya karbi hutun wata guda domin yayi kamfe. Shugaba Buhari ya yabawa APC da ta fitar da gwanin ta a tsanake cikin masu neman takara rututu inda yace Ministan na sa ya cancanci rike Ekiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel