Ayo Fayose zai gamu da uwar bari yayin da yake shirin barin kujerar Gwamna

Ayo Fayose zai gamu da uwar bari yayin da yake shirin barin kujerar Gwamna

- Gwamna Ayo Fayose na shirin barin kujerar Gwamnan Jihar Ekiti

- Ministan Buhari watau Kayode Fayemi zai sake takarar Gwamnan

- Ba mamaki dai a hurowa Ayo Fayose mai shirin barin gado wuta

Gwamna Jihar Ekiti kuma daya daga cikin manyan ‘Yan adawan Gwamnatin Buhari watau Ayo Fayose zai gamu kalubalen gaske yayin da wa’adin sa yake shirin karewa nan da ‘yan kwanaki kadan.

Ayo Fayose zai gamu da uwar bari yayin da yake shirin barin kujerar Gwamna

Gwamna Ayo Fayose na shirin barin gidan Gwamnati

Yanzu haka dai Jam’iyyar PDP da APC ta fitar da ‘Dan takarar ta a zaben Gwamna mai zuwa inda PDP ta tsaida Mataimakin Gwamna Fayose watau Farfesa Kolapo Olusoji yayin da APC ta tsaida tsohon Gwamna Dr. Kayode Fayemi.

Dele Momodu wani rikakken ‘Dan Jarida a kasar yace Mutanen Shugaba Buhari za su nunawa Gwamna Fayose cewa bai da wayau a dalilin rikakkar adawar da yayi da Gwamnatin. Momodu yace akwai yaki babba a gaban Gwamnan.

KU KARANTA: Jihohin da su ka fi kowane arzikin man fetur a Najeriya

Tuni dai har Shugaban kasa Buhari ya taya Ministan na sa watau Kayode Fayemi murnar lashe wannan kujera wanda haka ke nufin da-walakin. Momodu yace zai ma yi wuya Ayo Fayose ya cire kudin sa yayi wa Kolapo Olusoji kamfe.

Tuni dai tsohon Gwamnan na Ekiti watau Kayode Fayemi yace idan ya hau mulki zai daure Gwamna Ayo Fayose. Shi dai Fayose ya sha alwashin kara doke APC a zaben na bana.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel