‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma - Inji ‘Yan Shi’a

‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma - Inji ‘Yan Shi’a

- Mabiya Shi'a sun bara dangane da kwatanta su da akai da 'yan Boko Haram

- Jakadan kasar Amurka ne dai ya alakanta su da 'yan ta'addan Boko Haram din a wani bayani nasa

Shugaban yada labarai na ‘Yan uwa Musulmi da aka fi sani da Shi'a Ibrahim Musa, ya musunta tare da rushe zargin da tsohon Jakadan Amurka a Najeriya John Campbe ll yayi na alakanta mabiya darikar da kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram.

‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma-Inji ‘Yan Shi’a

‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma-Inji ‘Yan Shi’a

Tsohon Ambasadan ya yi wannan batun ne a ranar Asabar inda ya yi nuni da wasu kamanceceniya da mabiya darikar ke da shi da irin na kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram. Ya bayyana cewa ta bangaren abinda ya shafi shugabanci suna kama da juna, sai dai wannan batun nasa ya jawo cece-kuce.

Amma shugaban yada labarai na mabiyaShi’ar ya musunta wancan batu. Kana ya ce ko a baya shugaban nasu Sheik Al-zakzaky ya bayyana Boko Haram a matsayin wanda suka jawo koma baya ga danyen man fetur a yammacin Nahiyar Afrika.

KU KARANTA: ‘Yan Sanda na cigaba da rike Matar wani babban ‘Dan PDP a Borno

Har wa yau, idan aka yi duba da irin yadda kungiyar ta Boko Haram ta faro musamman nuna kiyayya ga ilimin boko, da kuma kawo karshen tasirin turawa a Najeriya da son kafa daular tsarin mulki irin nasu ya sha bam-bam da tsarin Shi’ar.

Ya kara da cewa, tabbas suna da bambamci musamman idan aka duba da irin gudunmawar da Sheik Zakzaky ya bayar wajen kawo dauki da karshen tashin hankali ya auku a shekara ta 2011, ga mabiya addinin kiristanci duk da cewa ba addini daya suke ba.

Ibrahim Musa ya cigaba da bayyana cewa "Duk wani yunkuri da za a yi wajen kwatanta mu da Boko Haram ba komai bane face bata suna ga darikar mu ta shi'a da kuma shugabanmu Shiekh Zakzaky."

‘Yan Shi’a dai suna cigaba da nuna adawa ga gwamnatin tarayya bisa rashin nuna halin ko in kula da kama shugaban nasu da ta yi a dalilin ricikin da ya auku tsakaninsu da wasu jami'an sojin kasar nan a watan Disambar shekara ta 2015.

A yanzu dai haka Sheikh Zakzaky ya shafe kwanaki har 882 a tsare ba tare da an gurfanar da shi gaban kotu domin yanke masa hukunci akan laifukan da ake tuhumarsa.

‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma-Inji ‘Yan Shi’a

‘Yan Boko Haram sunyi Gabas munyi yamma-Inji ‘Yan Shi’a

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel