To fa: Zai wahala Buhari ya kai bantansa a 2019 Inji Bafarawa

To fa: Zai wahala Buhari ya kai bantansa a 2019 Inji Bafarawa

- Manyan 'yan siyasa na cigaba da hasashen faduwar shugaba Buhari a zabe mai zuwa

- Wani jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana ta shi ma hangar dalilin da yasa talakawa ba zasu kara zabarsa ba

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Attahiru Bafarawa ya jadda cewa zai wahala Shugaba Buhari ya kai bantansa a zaben 2019 sakamakon gazawarsa wajen habbaka jindadi da walwalar yan Najeriya da yayi.

Bafarawa ya bayyana hakan ne a wata hira da yayi da gidan Radiyon Garkuwa, inda ya shaida cewa a tsawon mulkin Buhari ya kasa tabbatar da habakar tattalin arzikin kasar nan wanda hakan ya sanya rayuwa tayi tsanani ga mutane ga kuma matsalar tsaro da ta kara tabarbarewa a shekaru biyu da suka gabata.

Tsohon gwamnan ya ce “Bazan boye muku ba, a gani na aiki ne jawur sake cin zaben shugaba Muhammadu Buhari a 2019, sakamakon gaza cika alkawurran da ya dauka wanda ya sanya har talakawa suka zabe."

KU KARANTA: Yunwa, rashin Tsaro da Talauci duk gwamnatin Buhari ce ta kawo su - Sule Lamiɗo

Sannan ya ce, “Dama dai a ce ya cikawa talakawa alkawarin da ya daukar musu ne to da abin ya zo masa da sauki, amma maimakon haka ma sai kara tabarbarewa da lamarinsu yayi. A saboda haka a ganina bashi da wani dalili da zai sanya ya kara tasayawa takara.”

Bafarawa ya kuma kara da cewa, “Abu ne mai ciwo ganin yadda duk wadanda suka goyawa Buhari baya yaci zaben 2015 sun nisanta da shi yanzu, kamar irinsu Malam Buba Galadima da har yanzu Buharin bai ko kula shi ba tun da ya ci zabe."

Attahiru ya kuma bayyana cewa shi da kansa ya bayar da gudunmawa wajen tsayar da Buharin takara a jam’iyyar ANPP amma yanzu basa tare.

Da yake amsa tambayar ko zai fito takara a zaben 2019, sai yace, har yanzu bai yake shawara ba tsayawa ko a’a ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel