Alamu sun nuna: Tosohon gwamna Oshiomhole ne zai zama sabon angon jam’iyyar APC

Alamu sun nuna: Tosohon gwamna Oshiomhole ne zai zama sabon angon jam’iyyar APC

Akwai alamu masu karfi dake nuni da cewar jam’iyyar APC zata samu sabon shugaba ne ta hanyar sulhu, kamar yadda wasu majiya ta sanar da jaridar Punch a jiya, Asabar.

Za a gudanar da zaben sabin shugabannin jam’iyyar APC a watan Yuni mai zuwa bayan mahawara mai zafi a kan yiwuwar sabon zabe ko karawa shugabnnin jam’iyyar wa’adi zuwa 2019, bayan zabukan kasa da hukumar INEC zata gudanar.

Wani daga cikin shugabannin jam’iyyar masu barin gado ya tabbatar wad a jaridar Punch cewar, APC ta yanke shawarar samar da sabbin shugabanni da zasu jagoranci jam’iyyar ne ta hanyar sulhu.

Alamu sun nuna: Tosohon gwamna Oshiomole ne zai zama sabon angon jam’iyyar APC

Adams Oshiomhole

Majiyar ta shaidawa Punch cewar shugaba Buhari ya amincewa duk mai rike da mukami ya sake tsayawa takara idan yana da bukatar tazarce. Saidai shugaban jam’iyyar APC, Cif Odigie-Oyegun, ya bayyana cewar zai sauka daga kujerar domin bawa wasu dama.

DUBA WANNAN: 'Yan fashi sun tare hanyar Abuja-Kaduna, sun kashe dan sanda da wasu farar hula

Majiyar ta bayyana cewar za a lallami tsohon gwamnan jihar Kuros Riba, Cif Clement Ebri, dan takara daya tilo day a fito domin karawa da Oshiomhole, da yajanye takarar sa.

An gano cewar gwamnonin jam’iyyar APC na goyon bayan takarar Oshiomhole bayan ya fito karara, ranar Alhamis, ya bayyana niyyar sat a tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar APC. Kazalika shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC, Rochas Okorocha, ya bayyana cewar, Oshiomhole ne dan takarar gwamnonin jam’iyyar APC.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel