‘Yan Sanda na cigaba da rike Matar wani babban ‘Dan PDP a Borno

‘Yan Sanda na cigaba da rike Matar wani babban ‘Dan PDP a Borno

Kawo yanzu dai Jami’an tsaro na cigaba da tsare Iyalin wani ‘Dan siyasa da ke neman kujerar Gwamnan Jihar Borno a karkashin Jam’iyyar adawa na PDP watau Grema Terab. Kusan dai wata guda kenan da aka tsare matar dawasu Jama'a.

Sa’adatu Muhammad ta shiga hannun ‘Yan Sanda a tsakiyar watan jiya inda ake zargin ta da hannu cikin wani rikici da aka yi a Garin na Borno. Mijin na ta tace tun a lokacin aka dauke Matar sa da wasu daga cikin mutanen gidan sa.

‘Yan Sanda na cigaba da rike Matar wani babban ‘Dan PDP a Borno

An yi tir da tsare Matar Terab da Jami’an tsaro su ka yi

Terab wanda ya rike shugaban Hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Boro ya bayyanawa ‘Yan jarida wannan tun a watan jiya amma har yanzu Matar ta sa ta na tsare. An kama matar ne saboda wani rikicin siyasa da ya barke a cikin gidan sa.

KU KARANTA: Wasu Matsafa sun yi barna a cikin Garin Maiduguri

Grema Terab ya bayyana cewa Mai dakin ta sa na dauke da juna biyu lokacin da aka damke ta wanda har ta kai tayi bari a lokacin da ta kwana wajen ‘Yan Sanda. Jama’a da dama har da tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku sun yi tir da wannan lamari.

Abin ya kai gaban wani Kotu a Garin Maiduguri inda aka cigaba da rike Sa’adatu Muhammad a wajen ‘Yan Sanda. An dai nemi a bada beli, amma Kotu ta ki badawa har sau biyu. Jami’an ‘Yan Sanda dai sun ce aikin su ne ya kawo haka ba gabar siyasa ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel