Ziyarar Buhari zuwa Jigawa: An tura jami’an NSCDC 2,000

Ziyarar Buhari zuwa Jigawa: An tura jami’an NSCDC 2,000

Hukumar tsaro ta NSCDC ta bayyana cewar ta baza ma’aikatan ta 2,000 a fadin jihar Jigawa gabanin ziyarar kwanaki biyu da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai kai gobe.

Kakakin hukumar NSCDC a jihar Jigawa, SC Adamu Shehu, ya sanar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a Dutse, babban birnin jihar.

Kakakin hukumar ya bayyana cewar hukumar NSCDC a shirye take da ziyarar da Buhari zai jihar a gobe tare da bayyana cewar, sun tura jami’ai 2,000, wasu daga jihohin Kano da Bauchi, domin tabbatar da tsaro a yayin ziyarar shugaban kasar.

Ziyarar Buhari zuwa Jigawa: An tura jami’an NSCDC 2,000

Ziyarar Buhari zuwa Jigawa: An tura jami’an NSCDC 2,000

Shehu ya kara da cewa, an tura jami’an ya zuwa wurare na musamman da shugaba Buhari zai ziyartar a kwanaki biyun da zai yi a jihar.

DUBA WANNAN: An saki sakamakon zaben kananan hukumomin jihar Kaduna, karanta yadda ta kasance

"A wannan gaba ne nake son yin kira ga jama’a das u bawa jami’an mu goyon baya domin a yi taro lafiya a gama lafiya tare da bukatar jama’a su sanar da hukuma ko jami’an tsaro duk wani motsi na mutane da basu yarda da shi ba."

Kamfanin dillancin labarai na kasa ya rawaito cewar shugaba Buhari zai kaddamar da wasu hanyoyi da gwamnatin jihar Jigawa tayi a garuruwa biyar da kuma ragowar aiyukan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel