Ba wanda ya isa ya sa in ci amanar shugaba Buhari - Buratai

Ba wanda ya isa ya sa in ci amanar shugaba Buhari - Buratai

Hafsan sojojin kasa na Najeriya Laftanal Janar Tukur Buratai a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa ba wanda ya isa ya sa in ci amanar shugaba Buhari tare kuma da sake jadadda mubayi'ar sa ga shugaban kasar tare kuma da cigaba da yi masa biyayya hadi da kare demokradiyya.

Laftanal Janar Tukur Buratai wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Rasheed Yusuf ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake jawabin sa wajen taron farkon watanni uku na shekarar 2018 na rundunar sojin kasar a Abuja.

Ba wanda ya isa ya sa in ci amanar shugaba Buhari - Buratai

Ba wanda ya isa ya sa in ci amanar shugaba Buhari - Buratai

KU KARANTA: An gano dangantakar Buhari da Bishop Justin Welby

Legit.ng ta samu haka zalika cewa ya sake bayyana cewa shi da dukkan dakarun sa suna sane da irin gudummuwar da yakamata su rika bayarwa domin dorewar demokradiyya kuma ba za su yi kasa a gwiwa ba.

A wani labarin kuma, Wani labari mai taba zuciya da muka samu daga majiyar ya tabbatar mana da cewa wata sambaleliyar budurwa ta fara hauka tuburan biyo bayan dawowar ta daga wajen wani masoyin ta da ake kyautata zaton sa'ar mahaifin ta ne.

Kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu ta The Nation, lamarin ya auku ne a ranar 4 ga watan Mayun shekara ta 2018 a unguwar Ikenegbu ta karamar hukumar Sapele a jihar Delta dake kudu maso kudancin kasar nan.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel