Yan sandan Najeriya sun kama uba da dan sa bisa zargin yi wa 'yar shekara 10 fyade

Yan sandan Najeriya sun kama uba da dan sa bisa zargin yi wa 'yar shekara 10 fyade

Kotun majistare dake a garin Oredo na karamar hukumar Benin, babban birnin jihar Edo ta bayar da umurnin rufe wani uba mai suna Reuben Enosegbe, mai shekaru 50 a duniya da kuma dan sa mai suna Destiny dan shekaru 16 bisa laifin yi wa wata karamar yarinya fyade kamar dai yadda muka samu daga majiyar mu.

Ita dai yarinya wadda aka bukaci sakaya sunan ta da mummunan lamarin ya faru a kanta mun samu cewa tana da shekaru 10 ne kacal a duniya kamar dai yadda 'dan sanda mai gabatar da kara ya shaidawa kotun.

Yan sandan Najeriya sun kama uba da dan sa bisa zargin yi wa 'yar shekara 10 fyade

Yan sandan Najeriya sun kama uba da dan sa bisa zargin yi wa 'yar shekara 10 fyade

Legit.ng ta samu cewa sai dai dukkan wadanda ake zargin sun musanta hakan a gaban alkali.

A wani labarin kuma, Wani matashi a fusace dan kasar Ugandar nahiyar Afrika a cikin fushi ya kai beraye biyar da ya kama ya kuma sa a cikin mari a fishin 'yan sandan kasar yana mai tuhumar sa da lalata masa kudin ajiya.

Mutumin wanda majiyar mu ta ruwaito cewar sunan sa Peter Lojok Longolangiro dan kasuwa ne da yake ajiye kudaden sa a gida ba tare da kaiwa banki ba.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel