Tun da na hau mulki ban taba karbar albashi ba – Aregbesola

Tun da na hau mulki ban taba karbar albashi ba – Aregbesola

- Rauf Aregbesola bai taba karbar albashi ba tun da ya hau Gwamna

- Gwamnan na Osun yace Gwamnatin Jihar ta yi masa riga da wando

- Shekarar Aregbsola dai kusan 8 yana kan kujerar mulki a Jihar Osun

Mun samu labari cewa Gwamnan Jihar Osun Rauf Ogbeni Aregbesola na Jam’iyyar APC mai mulki bai taba karbar kudi daga hannun Gwamnatin Jihar sa ba da sunan albashin karshen wata.

Tun da na hau mulki ban taba karbar albashi ba – Aregbesola

Gwamna Aregbesola yace babu dalilin ya karbi albashi

Gwamna Rauf Ogbeni Aregbesola a wani jawabi da yayi a gidan Talabijin na TVC kwanan nan ya kara jaddada cewa bai taba karbar sisin kobo daga hannun Gwamnatin Jihar Osun da sunan albashi ba tun da ya hau mulki.

KU KARANTA: Kayode Fayemi zai sake neman takarar Gwamnan Ekiti

Rauf Ogbeni Aregbsola mai shekaru 60 yayi shekaru kusan 8 a kan mulki babu albashi. Gwamnan ya dare kujerar Gwamnan Jihar Osun ne a 2010 bayan Kotu ta soke zaben da Olagunsoye Oyinlola yayi nasara a zaben 2007.

Mai girma Gwamnan yace babu dalilin ya rika karbar albashi bayan Gwamnati ta tanadan masa wurin kwana mai kyau da kuma kudin magani. Bugu-da-kari Gwamnan yace ana kai sa duk inda ya ga dama a matsayin sa na Gwamna.

Wasu dai hakan ya ba su mamaki ganin irin facakar da Gwamnonin Kasar ke yi. Shi dai Gwamna Rauf Aregbesola yace ba sa da wani albashi a matsayin sa na Gwamna.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel