Tinubu ya sharhi a kan mutane da abubuwan da suka haddasa rikici yayin zabukan jam’iyyar APC

Tinubu ya sharhi a kan mutane da abubuwan da suka haddasa rikici yayin zabukan jam’iyyar APC

Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce rigingimun da aka samu a zabukan shugabannin jam’iyyar APC da aka gudanar karshen makon satin jiya sun faru ne sakamakon cushen ‘yan takara da wasu suka so yiwa jama’a.

Tinubu ya bayyana hakan ne a jiya, Asabar, yayin jawabi a wurin wani taron jam’iyyar APC. Tinubu ya bayyana cewar dole ne APC ta gudanar da zabukan cikin gida domin kare mutunci da manufofin tan a dimokradiyya.

Wasu mutane ne dake son karkatar da jam’iyyar APC daga kan manufar ta a siyasance. Suna da burin yin cushen yaran su a mukamai domin biyan bukatar kan su, wasu kuma na burin dawwama a mukaman su ta kowanne hali duk da kasancewar su zaben su aka yi ta halastacciyar hanya,” a cewar Tinubu.

Tinubu ya sharhi a kan mutane da abubuwan da suka haddasa rikici yayin zabukan jam’iyyar APC

Bola Tinubu

Tinubu ya bayyana cewar tun farko saida aka tafka mahawa tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar a kan batun gudanar da zaben shugabannin kafin daga bisani shugaba Buhari ya dauki mataki mafi wuya, na gudanar da zabukan, wanda, a cewar Tinubu, hakan shine mafi dacewa da tsari na dimokradiyya ta gaskiya.

DUBA WANNAN: Jam'iyyun Najeriya zasu yiwa shugaba Buhari rubdugu a zaben 2019

Duk da kasancewar an gudanar da zabukan lafiya, akwai wuraren da aka yi ba daidai ba tare da bayyana cewar an samu matsalolin ne saboda wasu masu iko a jam’iyyar a wasu jihohi na son ganin jam’iyyar ta koma mallakin su,” a cewar Tinubu.

Tinubu, tsohon gwamnan jihar Legas, ya kara da cewar, “ina fatan irin wadan nan ‘yan siyasa zasu gyara halayen su domin kishin jam’iyya, siyasa da kuma gyara sunan su a wurin jama,a."

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel