Ministan Lafiya ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ke neman Lafiyar sa a Kasashen Turai

Ministan Lafiya ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ke neman Lafiyar sa a Kasashen Turai

Ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewole, ya gaza ambata rashin aikata daidai da caccakar shugaban kasa Muhammadu Buhari dangane da neman lafiyar sa da yake ta faman yi a birnin Landan na kasar Birtaniya.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne shugaba Buhari ya dawo daga tafiyar sa ta neman lafiya wajen ganin likitocin sa a birnin Landan.

Ministan Lafiya ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ke neman Lafiyar sa a Kasashen Turai

Ministan Lafiya ya bayyana dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ke neman Lafiyar sa a Kasashen Turai

Mallam Garba Shehu, babban hadimin shugaban kasa akan hulda da manema labarai ya bayyana cewa, ubangidan na sa ya yiwa wannan balaguro ne sakamakon bukata da likitocin sa suka bayyana yayin tsaiko na duba lafiyar jirgin sa yayin da yake kan hanyarsa daga birnin Wasington inda ya gana da shugaban kasar Amurka, Donald Trump.

KARANTA KUMA: Shugaba Buhari ya yi alkawarin daidaita tsarin Jami'o'in Najeriya

A yayin ganawa da kafar watsa labarai ta Channels TV, Ministan ya bayyana cewa ta yiwu shugaba Buhari ya zabi likitocin kasashen waje ne domin boye sirrinsa kamar yadda ku san kowane dan Najeriya ke kokarin sirranta yanayi na lafiyar sa.

Farfesa Adewole ya jaddada cewa, neman lafiyar da shugaba Buhari ke yi a birnin Landan ba ya nufin nuna rashin ingancin harkokin lafiya na kasar nan.

Ya kara da cewa, ko kada shugaba Buhari bai aikata ba daidai ba kasancewar yana da dama kamar kowane dan Najeriya wajen neman lafiyar sa a duk inda ya bukata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel