Rubdugu: PDP, sabuwar jam’iyyar Obasanjo da wasu jam’iyyu 38 na yiwa Buhari wani yakin sunkuru

Rubdugu: PDP, sabuwar jam’iyyar Obasanjo da wasu jam’iyyu 38 na yiwa Buhari wani yakin sunkuru

A kokarin sun a ganin sun karbi mulki daga hannun shugaba Buhari da jam’iyyar APC a shekarar 2019, jam’iyyun adawa dake Najeriya zasu yi wata ganawa cikin kwanakin nan domin hada karfi wuri guda domin goyon bayan dan takarar shugaban kasa guda daya.

Wasu daga cikin jam’iyyun da zasu kasance cikin tattaunawa akwai sabuwar jam’iyyar Obasanjo (ADC), Jam’iyyar SDP ta Cif Olu Falae da sauran su.

Tuni kungiya mai rajin ceton Najeriya ta IMN karkashin jagorancin Dakta Olisa Agbakoba da Dakta Abduljalil Tafawa-Balewa ta fara ganawa da wasu jam’iyyun Najeriya 35 domin dunkulewa wuri guda kafin zaben 2019 kamar yadda jam’iyyar ta tabbatar a wata sanarwa.

Rubdugu: PDP, sabuwar jam’iyyar Obasanjo da wasu jam’iyyu 38 na yiwa Buhari wani yakin sunkuru

Rubdugu: PDP, sabuwar jam’iyyar Obasanjo da wasu jam’iyyu 38 na yiwa Buhari wani yakin sunkuru

Kungiyar zata yi wata ganawa ta musamman da jam’iyyar SDP cikin satin da zamu shiga.

Tsohon shugaban kasa Obasanjo da kungiyar sa sun dunguma sun shiga sabuwar jam’iyyar ADC kamar yadda jagoran kungiyar day a kafa ta kasa, Plagunsoye Oyinlola, ya sanar.

DUBA WANNAN: 'Yan sanda sun budewa magoya bayan jam'iyyar APC wuta a jihar Ribas

Wata majiya dake da kusanci da Obasanjo ta bayyana cewar, shigar Obasanjo sabuwar jam’iyyar ya farkar da wasu daga dogon bacci da suka shiga kuma har sun fara tuntubar jam’iyyar domin hada karfi wuri guda tare da fuskantar zaben 2019.

Da aka tambayi majiyar ko mai yasa basa tunanin kwatsewa guda kamar yadda jam’iyyar APC tayi kafin zaben 2015, sai ya bayyana cewar babu lokaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel