An zabi ‘Yar Najeriya zuwa wajen wani taro na yara masu basira a Duniya

An zabi ‘Yar Najeriya zuwa wajen wani taro na yara masu basira a Duniya

Wata yarinya ‘yar baiwa mai shekaru 12 tak a Duniya a Najeriya ta samu gudumuwar makudan kudi da sun kusa kai Naira Miliyan 1.5 domin halartar wani taro da za ayi a Amurka kwanan nan.

Oluwatomisin Jasmin Ogunubi yarinya ce mai tsananin basira wanda ta samu kyautar Dala $4000 daga bankin Keystone na Najeriya domin samun daman halartar wani taro da za ayi na yara masu hazaka da ake ji da su a Duniya a Kasar Amurka.

An zabi ‘Yar Najeriya zuwa wajen wani taro na yara masu basira a Duniya

Yarinya mai shekara 12 ta samu gudumuwar $4000

Tomisin ta samu damar halartar wannan taro ne saboda basirar ta don haka ne bankin na Keystone ya ya bata gudumuwar wannan kudi. Wani babba a Bankin Obeahon Ohiwerei yace wannan yana cikin kokarin su na karfafawa yara masu hazaka.

KU KARANTA: Likitoci 10, 000 za su bar Najeriya kafin shekarar 2023

Wannan yarinya Oluwatomisin Jasmin tun tana karamar ta dai ta kirkiro wata manhaja da za ta rika bayyana inda yara su ka shige. Dalilin haka ta ci kyauta iri-iri a Kasashen Duniya irin su Kasar Amurka da Ingila da kuma Kasar Kanada.

Oluwatomisin mai shelara 12 dai za ta halarci wannan gagarumin taro da Jami’ar Yale ta Amurka ta shirya tare da sauran ‘Yan uwan ta Hazikan Duniya. Yanzu haka tana karatu ne a wata Makarantar mata a Legas mai suna “Vivian Fowler Memorial College”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel