Osinbajo ya halarci bikin rantsar da shugaban Kasar Sierra Leone

Osinbajo ya halarci bikin rantsar da shugaban Kasar Sierra Leone

A ranar Asabar din da ta gabata ne mataimakin shugaban Farfesa Yemi Osinbajo ya shilla daga birnin Abuja zuwa birnin Freetown na kasar Sierra Leone domin halartar bikin rantsar da shugaban ta, Julius Bio.

Mun samu wannan rahoto da sanadin wata sanarwa ta Mista Laolu Akande, babban hadimin Osinbajo akan hulda da manema labarai, inda ya bayyana cewa tafiyar ubangidan na sa ta wuni guda da ya dawo a jiya Asabar.

Shugaba Julius Bio ya lashe zaben kujerar shugaban kasar ta Sierra Leone da aka gudanar a ranar 31 ga watan Maris.

Osinbajo ya halarci bikin rantsar da shugaban Kasar Sierra Leone

Osinbajo ya halarci bikin rantsar da shugaban Kasar Sierra Leone

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, shugabannin kasashen Guinea, Liberia, Ivory Coast, Senegal, Burkina Faso da kuma na Gambia sun halarci wannan bikin na rantsuwar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: An kashe 'Yan ta'adda 18, 56 sun shiga hannu a jihar Kaduna

Legit.ng da sanadin shafin jaridar The Punch ta fahimci cewa, wasu mashahurin 'yan wasan kwaikwayo na Nollywood sun halarci bikin da suka hadar da Omotola, Jalade, Mercy Johnson, Osita Iheme da kuma John Okafor da ya shahara da sunan Mista Ibu.

Rahotannin sun bayyana cewa, shahararren mawakin na Najeriya, Davido, ya halarci wannan biki a birnin na Freetown.

A yayin haka kuma jaridar Guardian ta ruwaito cewa, wannan biki ya ci karo da ranar haihuwar shugaban kasar da ya cika shekaru 56 a duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel