2019: Shugaba Buhari ya shirya tsaff don fara kamfe, ku fito a kara - Hadiminsa ga 'yan adawa

2019: Shugaba Buhari ya shirya tsaff don fara kamfe, ku fito a kara - Hadiminsa ga 'yan adawa

Babban mataimakin shugaban kasa na yada labarai, Malam Garba Shehu, a ranar juma'a, 11 ga watan Mayu, ya kalubalanci jam'iyyar hamayya akan fitowa takarar shugaban kasa Muhammadu Buhari zaben 2019.

2019: Shugaba Buhari ya shirya tsaff don fara kamfe, ku fito a kara - Hadiminsa ga 'yan adawa

2019: Shugaba Buhari ya shirya tsaff don fara kamfe, ku fito a kara - Hadiminsa ga 'yan adawa
Source: Twitter

Legit.ng ta Samu rahoton cewa Garba yayi magana a Abuja bayan dawowar shugaban kasar daga kasar Landan inda yaje duba lafiyar shi.

Yana cewa: 'Kamar yanda kuka gani shugaban kasa ya dawo, awa ashirin da hudu kafin yanda ya tsara.

Wannan na nuna muku cewa, babu wani abun damuwa kamar yanda muka sanar daku da farko. Amma wannan siyasa ce kuma muna amfani da damar nan don mu sanar da masu hamayya cewa su shiryawa zaben 2019.

Shugaban kasar ya tabbatar da cewa yaje Amurka don duba lafiyar shi. Yace :"Naje don duba lafiya ta ne. Kalau nake."

DUBA WANNAN: Zabukan Kaduna basu yi wani armashi ba

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tsara dawowa ne a ranar asabar amma sai ya iso da yammacin juma'a, 11 ga watan Mayu. Ya dawo ne daga duba lafiyar shi a tafiyar kwana hudu da yayi zuwa birnin Landan.

Shugaban ya sauka ne a filin jirgin Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya, Abuja da karfe 6:49 na yamma.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel