An kashe 'Yan ta'adda 18, 56 sun shiga hannu a jihar Kaduna

An kashe 'Yan ta'adda 18, 56 sun shiga hannu a jihar Kaduna

Kimanin 'yan ta'adda 18 ne suka rasa rayukan su tare da 56 da suka shiga hannu yayin gudanar wani aiki na hukumar 'yan sanda a jihar Kaduna.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana, ana zargin wannan 'yan ta'adda da laifukan kashe-kashe gami da garkuwa da mutane a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar da kuma wasu sassa na yankunan dake makwabtaka da jihar Zamfara.

Kakakin hukumar 'yan sanda na kasa, Mista Jimoh Moshood

Kakakin hukumar 'yan sanda na kasa, Mista Jimoh Moshood

Hukumar 'yan sandan ta bayyana cewa, watanni biyu da suka gabata ne ta samu nasarar cafke wasu 'yan baranda da ake zargin su da kashe wasu ma'aikatan tsaro na garin na Birnin Gwari.

An gabatar da wannan 'yan ta'addda da suka shiga hannu ga manema labarai a ofishin 'yan sanda na Katari dake jihar ta Kaduna.

KARANTA KUMA: Mun warware Matsalolin mu da Obasanjo ya Kalubalanta - PDP

Kakakin hukumar 'yan sanda na kasa Mista Jimoh Moshood ya bayyana cewa, 'yan ta'adda sun shiga hannu sakamakon jarumta ta jami'an tsaro karkashin jagoranci Sufeto Janar na 'Yan sanda da manufar sa ta kawo karshen afkuwar hare-hare a jihar.

Mista Moshood ya kara da cewa, an kama wannan 'yan ta'adda ne tare da muggan makamai gami da motocin su 11 a yayin musayar da aka sha fama har na tsawon sa'o'i na fafatawa tsakanin su da jami'an tsaro.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel