An damke yan baranda a wajen zaben fidda gwani a jihar Ekiti

An damke yan baranda a wajen zaben fidda gwani a jihar Ekiti

Jami’an hukumar yan sanda sun damke wasu yan baranda a wajen zaben fidda gwanin jam’iyyar APC domin takara a zaben kujeran gwamnatin jihar da za’ayi a watan Yuli.

Yan barandan sun yi fito-na-fito da jami’an yan sanda saboda sun hanasu shiga wajen zaben sakamakon rashin gabatar da takardun shiga taron.

Daya daga cikinsu ya zo wajen kunshe da kayan tsubbu ya fuskanci da jami’an tsaro. Bai cutar da kowa ba. An damke guda 4 daga cikinsu.

An damke yan baranda a wajen zaben fidda gwani a jihar Ekiti

An damke yan baranda a wajen zaben fidda gwani a jihar Ekiti

Yan barandan sun yi ikirarin cewa su mambobin jam’iyyar ne kuma suna da hakkin shigaba wajen amma basu da takardun shaidan da ke tabbatar da hakan.

KU KARANTA: An harbe wani harbe a zaben jam’iyyar APC

A makon da ya gabata, anyi rikici a zaben fiddan gwanin jam’iyyar APC na takaran kujeran gwamnan jihar Ekiti. Shugaban kwamitin zaben kuma gwamnan jihar Nasarawa, Tanko Al Makura, ya bayyana cewa yau Asabar za’a cigaba da zaben kuma akwai isassun jam’ian tsaro.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel