Da dumi-dumi: An harbe wani a zaben jam’iyyar APC

Da dumi-dumi: An harbe wani a zaben jam’iyyar APC

Legit.ng ta samu rahoton cewa wani mutum ya rasa ransa sanadiyar harbin bindiga a zaben shugabannin jam’iyyar APC na kananan hukumomi a jihar Legas.

Mamacin mai suna, Nurudeen Olanose, ya sha harsashi ne a makarantan Centra, Dopemu yayinda wani hatsaniya bayan an kamala zaben.

Wasu mutane 2 sun jikkata kuma jami’an tsaro sun damke mutane 9 tattare da wannan kisa kuma an kaisu ofishin yan sandan unguwar Agege.

Wani idon shaida ya bayyanawa jaridar Premium Times cewa rikici ya barke ne yayinda kakakin majalisar dokokin jihar Legas, Mudashiru Obasam ya iso filin zaben.

KU KARANTA: Ma’aikatan lafiyan Najeriya su na tserewa zuwa UK, US, UAE da Kanada

Yace: “Obasa ya zo wajen zaben a Dopemu, kawai sai aka ji harbin bindiga wanda ya kashe mamban jam’iyyar daya. Sai dogaransa suke jefar da gawan gefe daya sannan ya arce daga wajen.”

“Bayan minti goma kuma, yaran Obasa suka kashe wani kuma, sannan aka harbi wani a kafa.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel