Yadda zan karfafawa ‘Yan kasuwa idan aka zabe ni a 2019 - Atiku

Yadda zan karfafawa ‘Yan kasuwa idan aka zabe ni a 2019 - Atiku

- Atiku Abubakar ya fadi yadda zai dafawa masu kokarin kasuwanci

- Babban ‘Dan siyasar yace dole fa kasa ta rika tafiya da ‘Yan kasuwa

- Ba mamaki Tsohon Mataimakin Shugaban kasar ya fito takara a PDP

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana yadda zai babbako da tattalin arzikin Najeriya idan har ya samu damar zama Shugaban kasar nan a zabe mai zuwa.

Yadda zan karfafawa ‘Yan kasuwa idan aka zabe ni a 2019 - Atiku

Wazirin Adamawa Atiku ya fadi yadda za a dafawa 'Yan kasuwa
Source: Depositphotos

Festus Edomwande ya nemi jin ta bakin Atiku Abubakar da kan sa domin jin yadda zai taimakawa ‘Yan kasuwan da ke sana’a cikin halin ka-ka-ni-ka-yi. Atiku Abubakar kuwa nan take ya sa amsa a shafin sa na Tuwita.

‘Dan takarar Shugaban kasar a zabukan da su ka wuce yace dole a rika tafiya da ‘Yan kasuwa domin su ne kashin tattalin arzikin Kasa. Atiku Abubakar yace idan ana so ayi nasara dole a ba su makamashin aiki a Kasar.

KU KARANTA: Mataimakin Shugaban kasa ya kasa shawo kan rikicin APC

Babban ‘Dan siyasar ya kara da cewa idan ya samu mulki zai bada damar samun jari domin karfafa kasuwanci sannan kuma ya bada damar kowa ya baza kasuwancin sa. Ba mamaki Atiku dai ya tsaya takarar Shugaban kasa a PDP.

Wazirin na Adamawa Alhaji Atiku Abubakar ya kuma ce Gwamnati ba za ta rika shi cikin harkar ‘Yan kasuwa ba wanda yace hakan ne zai taimakawa masu kokarin tasowa. Kwanaki wasu Matasa sun ce za su marawa Atiku baya a 2019.

Wazirin Adamawa kuma Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana yadda zai babbako da tattalin arziki idan ya samu mulki. Atiku Abubakar ya dage wajen neman kujerar Shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel