An gano dangantar shugaba Buhari da babban malamin addinin kirista Bishop Justin Welby

An gano dangantar shugaba Buhari da babban malamin addinin kirista Bishop Justin Welby

Ko shakka babu kusan dukkan masu bibiyar lamurran shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari zasu fahimci cewar lallai akwai wata alaka mai karfi tsakanin sa da babban malamin addinin kirista din nan kuma Bishop na kasar Birtaniya mai suna Justin Welby musamman ma ganin cewa suna yawan haduwa.

Wannan ne ma ya sanya muka dage bincike har sai da muka gano wani rahoto da kafar sadarwar zamani ta gidan Talabijin mai lakanin jam'iyyar APC watau All Progressives Congress TV news ta wallafa game da hakan.

An gano dangantar shugaba Buhari da babban malamin addinin kirista Bishop Justin Welby

An gano dangantar shugaba Buhari da babban malamin addinin kirista Bishop Justin Welby

KU KARANTA: Yan sanda sun kama wani malamin addini bisa zargin satar yaro

Legit.ng ta samu cewa a cewar su All Progressives Congress TV news din dai shine amintakar shugaban kasar Muhammadu Buhari da shi Justin Welby ta fara ne tun a kusan shekarun 1970 da 'yan doriya lokacin da shugaban kasar na ministan albarkatun mai.

A cewar ta su, shima Justin Welby a lokacin yana shugabantar hukumar albarkatun man ne na wani babban kamfanin kasar Faransa mai suna Elf Aquitaine dake kula da shiyyar yammacin Afrika ciki kuwa hadda Najeriya inda ma babban ofishin sa yake a garin Abuja.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel