Namu-ya-samu: Hukumar NNPC za ta fara hako mai daga rijiyoyi 4 a Arewa

Namu-ya-samu: Hukumar NNPC za ta fara hako mai daga rijiyoyi 4 a Arewa

Shugaban rukunin kamfanonin dake tu'ammali tare da sarrafa albarkatun danyen mai na gwamnatin tarayyar Najeriya watau Nigerian National Petroleum Company (NNPC) mai suna Dakta Maikanti Baru ya sanar da cewa za su fara aikin hako mai daga yankin Gongola a arewa.

Yankin Gongola dai yanzu haka ya hada da jahohin Adamawa, Taraba da kuma wani yanki na Bauchi duka dai daga shiyyar Arewa maso gabashin kasar nan.

Namu-ya-samu: Hukumar NNPC za ta fara hako mai daga rijiyoyi 4 a Arewa

Namu-ya-samu: Hukumar NNPC za ta fara hako mai daga rijiyoyi 4 a Arewa

Legit.ng ta samu cewa Dakta Maikanti Baru ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a wajen taron lacca da jami'ar Abubakar Tafawa Balewa University (ATBU) ta shiya a garin Bauchi.

Kamar dai yadda muka samu, kamfanin na NNPC zai yi aikin hakar man ne daga rijiyoyin da suka hada da tafkin Kolmani -1, Nasara-1 da kuma Kuzari-1 in 2018.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel