Mun warware Matsalolin mu da Obasanjo ya Kalubalanta - PDP

Mun warware Matsalolin mu da Obasanjo ya Kalubalanta - PDP

Jam'iyyar adawa ta PDP ta bayyana cewa, a halin yanzu ta tsarkaka daga duk wani kalubale da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ke yi a kanta sakamakon sabon salo na managarcin jagoranci gami da tsarkakan tsare-tsare.

A ranar Juma'ar da ta gabata ne Jam'iyyar ta bayar da wannan tabbaci da sanadin kakakin ta, Mista Kola Ologbondiyan a babban birnin tarayya na Abuja.

Kakakin jam'iyyar ya bayyana cewa, sabbin tsare-tsare gami da sauye-sauye da jam'iyyar PDP ta shimfida a halin yanzu za su tabbatar da cikar burika da biyan bukatun 'yan Najeriya dangane duba da karatowar zaben 2019.

Ologbondiyan yake cewa wannan tsare-tsare za su tabbatar al'ummar kasar nan sun sharbi romom dimokuradiyya a sakamakon sabon salo na tsarkakken jagorancin jam'iyyar su ta PDP.

Kakakin Jam'iyyar PDP; Mista Kola Ologbondiyan

Kakakin Jam'iyyar PDP; Mista Kola Ologbondiyan

A kalaman sa, "cikin watanni biyar da suka gabata gabanin zuwan sabon shugabanci karkashin jagorancin Prince Uche Secondus, jam'iyyar PDP ta dauki wani salo na tsarkake kanta sakamakon daukar shawarwari da korafe-korafen 'yan Najeriya."

"A sanadiyar wannan tsarkaka ya sanya jam'iyyar ta gudanar da zaben fitar da dan takarar gwamnan jihar Ekiti cikin lumana ba tare da wata kwayar zarra ta magudi ba."

Mista Ologbondiyan ya yabawa kanwa uwar gamin matsalolin jam'iyyar su, gwamnan jihar Bayelsa, Seriake Dickson, wajen sulhunta duk wani rikici da kwantar da tarzoma wanda a da can tayi kaka-gida cikin jam'iyyar.

KARANTA KUMA: Taron Jam'iyya: Okorocha da shugabannin APC na Jihar Imo sun gana da Osinbajo

Ya ci gaba da cewa, wannan tsarkaka ta jam'iyyar ya sanya dumbin al'umma su ka yi tiririya ta goyon baya yayin gudanar da tarukan ta a jihohin Katsina, Jigawa da kuma Osun.

Ya kara da cewa, babbar manufa ta jam'iyyar wadda ta sanya a gaba ita ce habakar tattalin arziki da zai ciyar da kasar nan gaba.

A yayin haka kuma kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, a kwana-kwanan nan ne mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bayyana karara cewa babu wata jam'iyya da ka iya ceto kasar nan daga cikin kangi na matsalar tattalin arziki a halin yanzu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel