Gwamnatin Tarayya ta biya N439m ga mutane 14 da suka Busa Usir kan marasa biyan Haraji

Gwamnatin Tarayya ta biya N439m ga mutane 14 da suka Busa Usir kan marasa biyan Haraji

Da sanadin shafin jaridar Vanguard mun samu rahoton cewa, gwamnatin tarayya ta biya Naira Miliyan 439.276 ga mutane 14 da suka yi tonan silili da fallasa kan masu kudundune kudaden su wajen rashin biyan haraji a kasar nan.

Ministan Kudi ta kasa, Misis Kemi Adeosun, ita ta bayyana hakan a yayin ganawa da manema labari a birnin tarayya na Abuja a ranar Alhamis din da ta gabata.

Misis Adeosun ta bayyana cewa, masu busa usir 14 sun dakumi kudaden su cikin wannan mako yayin da gwamnatin tarayya ta tura Naira biliyan 13.8 cikin asusun ta na kudaden haraji da ta karbo daga hannun masu danne hakkin kasar nan.

Legit.ng ta fahimci cewa, a watan Dasumba na shekarar 2016 da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta kafa wannan sabuwar doka ta biyan masu fallasa danniyar hakkin ta ta hanyar kudundune haraji da duk wani nau'i na zamba da rashawa.

KARANTA KUMA: Hukumar Sojin Sama ta kaddamar da wani Sabon Rukuni a Jihar Osun

Rahotanni sun bayyana cewa, wannan sabuwar doka ta taka rawar gani wajen azurta mutane 14 da N439m cikin makon da ya gabata sakamakon busa usir da suka yi akan masu kauracewa biyan haraji a kasar nan wanda mafi akasarin su kamfanoni ne da masana'antu.

Bayan bincike na diddigi cikin wannan tonan asiri da mutane 14 suka aiwatar, gwamnatin tarayya ta kwato hakkin ta na haraji na kimanin N13.8bn wajen masu kauracewa biyan ta inda ta tabbatar da shigar kudaden cikin asusun ta da sanadin hukumar haraji ta kasa watau FIRS.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel