Kwamitin raba Zakkah ta tallafawa marasa lafiya da kudi naira miliyan 6 da rabi

Kwamitin raba Zakkah ta tallafawa marasa lafiya da kudi naira miliyan 6 da rabi

Kwamitin bada zakkah ta jihar Sokoto ta bawa majinyatan jihar tallafin Naira miliyan 6 da rabi. Shugaban kwamitin, Malam Lawal Maidoki, yayi jawabi a yayin raba tallafin, yace tallafin an bada shine ga wadanda basu da karfin siyan magani

Kwamitin raba Zakkah ta tallafawa marasa lafiya da kudi naira miliyan 6 da rabi

Kwamitin raba Zakkah ta tallafawa marasa lafiya da kudi naira miliyan 6 da rabi

Kwamitin bada zakkah ta jihar Sokoto ta bawa majinyatan jihar tallafin Naira miliyan 6 da rabi. Shugaban kwamitin, Malam Lawal Maidoki, yayi jawabi a yayin raba tallafin, yace tallafin an bada shine ga wadanda basu da karfin siyan magani.

DUBA WANNAN: Da Ango yaje zaike ma 'yar mitsilar Amaryarsa, ta halaka shi, leka kuji me take gaya wa kotu

An rarraba kudin ga kwamiti daban daban na asibitoci da kuma dakuna shan magunguna a fadin jihar.

Asibitin kwararru ya samu Naira miliyan 1.5, a inda asibitin koyarwa na jami'ar Usmanu Danfodiyo ya samu Naira miliyan 1 sakamakon yajin aikin JOHESU.

Maidoki da alhini yace, wasu daga cikin masu matsalar kwakwalwa ma ma'aikatan dake yajin aiki sun koresu.

Shugaban kwamitin, wanda yayi Allah wadai da yajin aikin, ya bada shawarar kirkiro da dokar hana ma'aikatan lafiyar tarayya, jihohi da kananan hukumomi yajin aiki.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel