Nuna mana dan takararsa - Yahaya Bello ya kaluabalanci Obasanjo

Nuna mana dan takararsa - Yahaya Bello ya kaluabalanci Obasanjo

- Gwamna Yahaya Bello ya kalubalanci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mutanensa na siyasa dasu nunawa ‘yan najeriya dan takararsu na shugaban kasa

- Obasanjo ya kasance ya kirkira kungiyar siyasa, inda ya bayyana cewa zai fita daga kungiyar indai har suka hada kai da wata jam’iyya ko kuma suka bawa kansu suna suka koma matsayin jam’iyya

- Gwamna Yahaya Bello, yace duniya tana jiran taga dan takarar da jam’iyyar ADC zata tsaida wanda zai kasance yana daidai da shugaban kasa na yanzu

Gwamna Yahaya Bello ya kalubalanci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da mutanensa na siyasa dasu nunawa ‘yan najeriya dan takararsu na shugaban kasa, tinda har sun bude jam’iyya mai suna ADC wadda suke ganin zata iya ja da jam’iyyar gwamnati ta APC a 2019.

Obasanjo ya kasance ya kirkira kungiyar siyasa, inda ya bayyana cewa zai fita daga kungiyar indai har suka hada kai da wata jam’iyya ko kuma suka bawa kansu suna suka koma matsayin jam’iyya, yace shi yanaso ya kasance baba ga kowane dan jam’iyyar siyasa a Najeriya.

Nuna mana dan takararsa - Yahaya Bello ya kaluabalanci Obasanjo

Nuna mana dan takararsa - Yahaya Bello ya kaluabalanci Obasanjo

Amma a ranar Juma’a, a garin Lokoja, a zagayen masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC, gwamna Yahaya Bello, yace duniya tana jiran taga dan takarar da jam’iyyar ADC zata tsaida wanda zai kasance yana daidai da shugaban kasa na yanzu.

KU KARANTA KUMA: Wata yar Najeriya Ramota Lawal, ta zama kansila mafi yarinta a kasar Ingila

Gwamnan ya kara da cewa faduwar da akayi a zaben 2015 wasan yara ne ga jam’iyyun adawa, idan aka dan gantashi da wanda zasu fuskanta a shekarar 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel