Yanzu-Yanzu Wasu 'yan daba sun bankawa sakatariyar APC wuta a jihar Imo

Yanzu-Yanzu Wasu 'yan daba sun bankawa sakatariyar APC wuta a jihar Imo

Wasu mutane da ake zargin yan daba ne sun banka wuta a sakatariyar jam'iyyar APC da ke jihar Imo.

Jaridar the nation ta ruwaito cewa kayayaki da dama sun kone a ofishin kuma a halin yanzu da ake rubuta wannan rahoton ma'aikatan kashe gobara basu iso wurin ba.

Ciyaman din jami'iyyar na jihar, Hilary Eke, ya tabbatar da afkuwar lamarin a lokacin da manema labarai suka tuntube shi.

Yanzu-Yanzu Wasu 'yan daba sun bankawa sakatariyar APC wuta a jihar Imo

Yanzu-Yanzu Wasu 'yan daba sun bankawa sakatariyar APC wuta a jihar Imo

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari ya dawo gida Najeriya

"Na shigar da kara zuwa ofishin Sufeta Janar na hukumar Yan sanda bayan harin da aka kai wa sakatariyar ranar Asabar da ta gabata. Na yi abinda ya kamata inyi, sauran binciken kuma na hukumar yan sanda ne," inji shi.

A dai cikin 'yan kwanakin nan, jam'iyyar APC na jihar Imo tana fuskantar yan wasu matsaloli tun bayan taron shiyoyi da aka gudanar inda wasu mutane da ba'a san ko su wanene ba suka kwace kayayakin aikin zaben.

Idan ba'a manta ba dai, Legit.ng ta ruwaito cewa gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bayar da umurnin a gurfanar da mambobin kwamitin da ake aike su kula da yadda za'a gudanar da zaben na ranar Asabar da ta gabata.

Okorocha ya dauki wannan matakin duk da cewa Ciyaman din jam'iyyar na jihar ya ce an gudanar da zaben lami lafiya a shiyoyi 305 da ke kananan hukumomi 27 da ke jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel